Da matasa za su riki fasahar AI da rayuwar su ta inganta-CITAD
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma (CITAD), ta ce fasahar AI na taka muhimmiyar rawa wajen kawo wa al’umma ci gaba mai dorewa a wannan zamani.
Babban daraktan cibiyar Malam Yunusa Zakari, ne ya bayyana haka yayin taron wayar da Kan Matasa kan amfani da fasahar zamani karo na 5.
Yace sun dauki wannan maudu’i ne domin wayar da kan matasa dangane da nuhimmanci da kuma amfanin da sabuwar fasahar ta (AI), ke da shi musamman a bangaren zabe da kuma kirga kuri’u, har ma da bayyana sakamakon zaɓen.
Ya ƙara da cewa, amfani da wannan sabuwar fasaha, zai gyara ayyukan gwamnati da kuma kawo sauyin da al’umma ke bukata, tare da sanya ayyukan gwamnatin shiga lungu da sako, ta yadda mutane za su fahimci abinda ake yi a Jihohin su.
A zantawar wakiliyar mu Nusaiba Muhammad Auwal da wasu mahalar ta taron sun bayyana gamsuwarsu matuƙa tare da yin farin ciki bisa ga ilimin da suka samu a tsawon kwanaki biyu na gangamin.