Ya kamata mu inganta kere-kere da fasahar zamani domin farfado da arewacin Najeriya
Shirin Arewa Tech Fest, wani shiri ne mai nuna muhimmancin gina tsarin fasahar kere-kere don samar da ayyukan yi, a wannan zamani an gudanar da bikin baje kolin na kwanaki biyu a jihar kano.
Taron mai taken Empowering Innovation for Economic Growth na da nufin ganowa da inganta kere-kere da fasahar zamani a arewacin kasar nan, kamar yadda Shugaban taron kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya bayyana.
El-Rufai ya sanar da cewa nan gaba za a gudanar da baje kolin a fadin jihohin arewacin kasar nan ciki har da babban birnin tarayya Abuja ya kuma bayyana cewa an zabi jihar Katsina domin daukar nauyin bikin baje kolin na shekarar 2025.
Da yake jawabi tun da farko, Mai Martaba Sarkin Kano, Mal Muhammadu Sunusi na biyu ya bayyana damuwarsa kan dubban matasan da basu da aikin yi a kasar nan, inda ya bayyana cewa matasan ba su da isashen shiri don juyin juya halin masana’antu na hudu, da fasahar kere-kere ta yi.
Sarkin ya jaddada bukatar fara koyar da yara fasahar kere-kere domin dorewar da dogaro da kai, kamar yadda Artificial Intelligence (AI) da na’urar mutum-mutumi ke saurin mamaye sassa daban-daban a duniya idan ba mu yi hankali ba, mutane na iya fara rasa ayyukan yi, in ji shi.
Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da su sa matasa su shiga harkar bunkasa fasahar kere-kere, wanda a tunaninsa zai taimaka wajen rage yawan marasa aikin yi a fadin kasar nan.
A nasa bangaran mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci gwamna Abba Kabir Yusuf da yake jawabi a wajen taron ya bayyana cewa Arewa Tech Fest ba wai wani biki ba ne kawai, wani dandali ne na kamfanoni masu tasowa don baje kolin basirarsu da kuma janyo hankalin masu zuba jari.
Wakiliyar mu Nusaiba Muhammad Auwal ta ruwaito mana cewa taron ya samu halattar manyan mutane na ciki da wajen jihar Kano.