Kwana biyu ne rak ya rage mu maka jam’iyyar NNPP a kotu_ kungiyar kare hakkin dan Adam
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam da wayar da kan jama’a, ta Awareness for Human Right and Charity Foundation ta sha alwashin maka jam’iyyar NNPP ta jihar Kano, a kotu, matuƙar ba’a samu masalaha ba kan ƙorafin da suka samu na zargin da wasu masu sha’awar tsayawa takarar Kansila a mazaɓar Ɗandago da Sani Mai Nagge da ke ƙaramar hukumar Gwale suka yi kan take musu haƙƙi wajen tsayar da ƴan takara a mazaɓun nasu.
Daraktan ƙungiyar a matakin ƙasa Kwamared Auwal Usman Awareness ne ya bayyana hakan, yayin wani taron manema labarai da ƙungiyar ta gudanar ranar Laraba a ofishinta.
Wannan na zuwa ne bayan da mai neman tsayawa takarar Kansila a mazaɓar Ɗandago Hadi Shehu Abubakar, da wasu ƴan takarar Kansila a mazaɓar Sani Mai Nagge su biyu wato Mahfouz Musa da Musa Muhammad, dukka a ƙaramar hukumar Gwale, suka shigar da ƙorafin su a ofishin ƙungiyar.
Masu ƙarar sun zargi cewar jam’iyyar ta NNPP ba ta yi musu adalci ba wajen mayar da su saniyar ware, wajen tsayar da ƴan takarar a mazaɓun nasu.
Kwamared Auwal Awareness, ya kuma ce tun bayan da suka karɓi ƙorafin ne suka rubutawa jam’iyyar takarda mai ɗauke da wa’adin kwanaki biyar kan tayi abinda ya dace ko kuma su gauraya a gaban kotu, wanda ya ce yanzu haka wa’adin nasu ya rage kwanaki biyu.
Da yake jawabi tun da farko tsohon ɗan takarar kansilan a mazaɓar Ɗandago Hadi Shehu Abubakar, amadadin sauran masu ƙorafin ya ce, an umarce su ne da suje su yi sulhu akan tsayar da ƴan takarar a baya, amma bayan sun tafi sai sukaji an sanar da ƴan takarar a mazaɓun nasu, a don haka ne suka yi duk mai yiyuwa amma jam’iyyar ta NNPP ba ta yi komai ba, hakan yasa suka shigar da ƙorafin nasu a ofishin ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin.
Shima anasa bangaran shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kano hashimu sulaiman dungurawa yace ba mutum daya bane yake tsayawa takara a mazaba a cikin jam’iyya sannan Kuma yace babu laifi dan sama da mutum goma sun fito takara an bawa mutum daya kuma sun same shi a ofishin da yayi musu bayani.
Ya ce damar su daya ce idan jam’iyyar NNPP bata musu adalci ba su tafi wata jam’iyyar.
Ko a baya-bayan nan dai an samu ƙorafe-ƙorafe daga ɓangaren wasu daga cikin ƴan ƴan takararkari kama daga na shugabancin ƙananan hukumomi zuwa kuma na kansila.
Wataƙila ma wannan ce tasa wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a gwamnatin jihar Kano suka fara ajiye muƙamansu irin su Abdullahi Tanka Galadanchi da ya ajiye muƙamin sa a baya-bayan nan, ko da dai yanzu haka zaben ƙananan hukumomin na ƙara tunkaro wa, wanda za’a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoban 2024.