Dan majalisar tarayya Ikra Aliyu Bilbis ya raba tallafin karatu ga dalibai 1048
Sanata Ikira Aliyu Bilbis ya bayyana haka a lokacin bada tallafi ga daliban a wani bikin da Aka yi a sakatariyar JB Yakubu Dr. Garba Nadama da ke Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Sanata Bilbis ya bayyana cewa shirin na daga cikin alkawuran da ya yi na taimakawa Dalibai don ci gaba da karatunsu, inda ya ba da tabbacin ci gaba da hakan a gaba.
Bilbis ya bayyana Ilimi a matsayin kashin bayan duk wani ci gaba, inda ya yi kira ga al’ummar Jihar Zamfara da su mallaki ilimin addinin Musulunci da na boko.
“A shekarar da ta gabata Santa Bilbis ya yi irin wannan shiri ga daliban mazabarsa ta” Ikira.
Ya yabawa Gwamnan Jihar Dauda Lawal bisa kokarinsa na ba da fifiko a fannin Ilimi, ya kuma yi kira gare shi da ya ci gaba da yin hakan.
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin Gusau Dr, Ibrahim Bello ya yabawa Sanatan bisa wannan karimcin ,ya kuma yi kira ga Dalibai da su yi amfani da allafin da aka ba su a hanyoyin da suka dace, ya kuma bukaci sauran ‘yan siyasa, da attajirai da su yi koyi da Sanata Ikira.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal, ya bayyana farin cikinsa da shirin, inda ya bayyana shi a matsayin abin farin ciki ga Dalibai da al’ummar Jihar, ya kuma ba da tabbacin cewa za su kara ba da dukkan goyon baya da taimakon da ya kamata ga bangaren Ilimi.