SARKIN KANO ALHAJI AMINU ADO BAYERO YA KAI ZIYARAR GANI DA IDO KAN YADDA GOBARA TA TASHI A KASUWAR KANTIN KWARI DAKE KANO
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya kai ziyarar jajantawa ‘Yan kasuwar Kantin jim kadan da dawowarsa daga ziyarar aiki Abuja.
Dubun dubatar masoya da magoya baya ne sukayi cincirundo domin raka mai Martaba Sarkin kasuwar ta Kantin kwari.
Da yake jajantawa wadanda suka gamu da iftila’in gobarar, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yayi addu’a tare da fatan Allah ya kiyaye afkuwar hakan nan gaba.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma godewa Jami’an Hukumar kashe gobara ta jihar Kano da Jami’an tsaro da Kungiyar Yan kasuwar da dai daikun al’uma bisa yadda suka bada taimaka wajan kashe gobarar.
Sarkin daga nan sai ya bukaci Yan kasuwa da sauran al’uma su cigaba da yin addu’oi domin kiyayewar afkuwar irin wannan iftila’i tareda neman samun sassaucin al’amura na rayuwar yau da kullum.