Matsalar ruwan sha a kwaryar birnin kano na ci gaba da ta’azzara
Izuwa yanzu alamu sun nuna cewa matsalar ruwan sha a kwaryar birnin kano cigaba take da ta’azzara mai makon samun sauki duk kuwa da kokarin da hukumomi ke ikirarin yi wajen shawo Kan matsalar.
Matsalar dai da alama ta kara kamari ne tun bayan da aka samu yankewar wutar lantarki a Arewacin Nigeria, inda hakan ke nuna samar da ruwan shan a kano ya ta’allaka ne kacokan akan wutar lantarkin da kamfanin rarraba hasken lantarkin shiyyar kano ke samarwa.
Wani mazaunin yankin Chiranci a karamar hukumar kumbotso yayi Mana bayanin matsanancin halin da suka shiga sanadiyyar wannan matsalar ta rashin ruwan Sha Inda yace tun karfe biyu na dare suke fitowa Kuma kafin ma suje Inda zasu dibi ruwan tafiya ce Mai nisa Amman a haka zasu tafi su debo ruwa Inda yace haka zakaga samari suna fita cikin daran domin debowa iyayen su ruwa dama yara kananu.
Yakara da cewa kullum suna cikin fargabar yadda zasu hi hanyar duba da cewa hanya ce da Yan raba suke tare mutane su musu kwacen waya sannan ga matsalar fadan daba da ake fama dashi gashi Kuma cikin daren ne kawai ake iya samun ruwan shi yasa muke fitowa domin debowa .
Yayi kira da gwamnatin kano da tallafawa al’ummar jihar kano ta kawo karshen matsalar ruwan Shan da Ake fama dashi a jihar ta kano.
Engr Garba Ahmed Bichi, shine Manajan Daraktan hukumar bada ruwan sha ta jihar kano, mun tun tubeshi domin Jin martanin Gwamnati to sai dai har yanxun da muke hada rahotan mu bai biyo kiran da muka masa ba.
To sai dai a wata tattaunawa da wakiliyar mu tayi dashi a baya Engr Garba Ahmed Bichi yace a kowane wata Gwamnan jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf na sahale musu lita Dubu 400 da 50 duk wata domin samar da ruwansha, harma yana ikirarin wani man ne yake tadda wani saboda wadatar ruwan shan.
Wannan na zaman gyara kayanka, dafatan hankalin hukuma zai Kai ga wannan matsala domin magance ta.
Al’umma dai na cikin matsalar rashin ruwan sha wanda da kudin ka ma ba samu za kayi ba sannan na debowar Kuma yana wahala duba da matsalar wutar lantarki da aka samu