Rikicin zaben Kananan Hukumomi a Kaduna da sauran wurare
Zabubbukan kananan hukumomi wadanda su ne ginshikin tsarin dimokuradiyya, galibi ana fuskantar kura-kurai da munanan ayyuka. A baya-bayan nan dai an gudanar da zabukan kananan hukumomi a Kaduna da sauran sassan Najeriya,an fuskanci kura-kuran da ba su dace ba, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan sahihancin gudanar da zaben.
Daya daga cikin abubuwan da suka fara nuna damuwa a lokacin zaben kananan hukumomi a Kaduna shi ne rashin daidaiton adadin sakamakon da aka fitar. A rumfunan zabe da dama dai, an samu sabanin ra’ayi tsakanin wadanda suka yi rajista, da adadin kuri’un da aka raba da kuma na ainihin kuri’un da aka kirga. Wadannan sabani sun sanya shakku kan sahihancin sakamakon da kuma yadda ake tafiyar da harkokin zabe.
Wasu masu sa ido kan zabukan masu zaman kansu sun bayyana cewa, a wasu yankuna da dama, an samu fitowar jama’a fiye da yadda aka gani a kasa. Irin wannan yanayi ya nuna cewa mai yiwuwa an yi magudi ko gyare-gyare ba bisa ka’ida ba don nuna goyon baya ga wasu ‘yan takara.